A Kenya wani dan gudun hijira daga Burundi Innocent Havyarimana, yana yi tare da saida sabulu tun daga shekarar 2015, yana bada gudunmawar yaki da COVID-19. Ya kara yawan sabulun tare da rage kudin siyarwa, don jama'a su iya saye su wanke hannayensu.
A Amurka wasu 'yan sama jannati sun sauka a cibiyar NASA dake jihar Florida, bayan wata tafiaya da suka yi zuwa duniyar wata da jirgin SpaceX mai cike da tarihi. Wannan shine karon farko da kamfanin mai zaman kansa ba gwamnati ba ya taba zuwa duniyar wata.
A can kasar Lesotho kuma, an rantsar da tsohon ministan kudi Moeketsi Majoro yau Laraba a matsayin sabon Firai minister, wuni guda bayan Thomas Thabane ya yi murabus sakamakon matsin lamba a kan dambarwar kisar matarsa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai mayar da rage kudin da Amurka ke ba hukumar lafiya ta duniya da yayi, ya za ma na dindindin, idan hukumar “ba ta kawo wani babban, ci ba, nan da kwana 30 masu zuwa.”
A Sudan ta Kudu an tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar, Riek Machar da uwargidansa, Angelina Teny, wacce ke rike da mukamin ministan tsaro, sun kamu da cutar Coronavirus.
A Burkina Faso ne aka sake mayar da mutum-mutumi na Thomas Sankara a babban birnin kasar Ouagadougou, bayan an sake siffanta mutum-mutumin hoton tsohon shugaban kasar wanda aka kashe a 1987.
Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran ya yi gargadin cewa dakarun kasar za su mayar da martani muddin Amurka ta dauki wani mataki a kan jiragen dakon man Iran da suke kan hanyar zuwa Venezuela. Iran da Venezuela duka suna karkashin takunkuman Amurka.
An sami fashewar sinadarai a masana’antu dake kusa da birnin Venice na Italiya in da hayaki da wuta suka tashi, abinda ya sanya hukumomi sukayi kira ga jama’a su kasance a gida, su rufe dakunansu da tagoginsu.
A kasar Guinea kuma, bayan da jama’a suka yi zanga zangar nuna gajiya da dokar takaita fita saboda COVID-19 inda mutum bakwai suka mutu, mazauna Kamsar da Dubreka sun fito kan tituna suna balle masallatai da suka dade a rufe tun watan Maris da kasar a ayyana dokar ta baci.
Najeriya: Faduwar farashin danyen mai a duniya sakamakon Coronavirus, ta sa kasar shiga cikin halin kakanika yi, sabo da irin dogaro da kasar tayi da kudaden shiga ta hanyar sayar da mai ga kasashen ketare.
A Burundi gwamnatin kasar ta kori shugaban hukumar lafiya ta duniya a kasar da masu taimaka mushi uku. Ba a bayar da Karin bayani ba.
A Isra’ila kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yaba mata a yau Laraba a matsayin kawa a yaki da coronavirus da kuma ayyukan Iran a yankin kana ya kyautata zaton samun nasara a tattaunawar zaman lafiya da Washington ke yi da Falasdinu da bai taci tura a baya.
A Jamhuriyar Nijer ministan harkokin cikin gida Mohamed Bazoum ya kai ziyara a kauyukan dake yammacin yankin Tillaberi inda aka kashe mutum 20 a ranar Asabar a wasu jerin hare hare.
A Senegal inda shugaba Macky Sall ya ba da sanarwa ta gidan talabijin cewa za a “sassauta” wasu dokokin da aka kafa na Coronavirus.
A kasar Madagaska, kasashen Afirka da dama suka sayi maganin gargajiya na Covid-19, maganin da aka yi shi daga itatuwa da shugaban kasar Andry Rajoelina ya ke alfahari da shi, duka da gargadin hukumar lafiya ta duniya WHO.
Iran ta ce a shirye ta ke ta tattauna da Amurka kan musayar fursinoni biyo saboda fargabar Korona Biros za ta iya jefa rayukan fursinonin cikin hadari, acewar kafar yada labarai ta gwamnatin Iran.
Domin Kari