Babban jami’in diflomasiyyar Turai, Josep Borrell ya ce nahiyar Turai ta "girgiza matuka" game da kisan bakar fata George Floyd a Amurka, sannan ya yi Allah wadai da "amfani da iko ba bisa ka’ida ba."
Fim din Cook Off na ‘yan Zimbabwe na labarin wata mata wadda ya samu karbuwa a lokacin gasar girki, shirin da aka haska a Netflix ranar Litinin, fitowar sa da ake fatan zai taimakawa karamar masana’antar fim din kasar ta samu masu kallo da yawa a duniya.
A kasar Zimbabwe, wadansu iyalai suna dandana kudarsu sakamakon matakan hana zirga zirga da aka dauka da nufin dakile yaduwar COVID 19, yayinda suke fadi tashi wajen neman abinda za su ci
A shirin Taskar VOA na wannan makon, za ku ji kiran majalisar dinkin duniya inda take neman agajin kimanin dala miliyan bakwai a duniya domin tunkarar mayuyacin yanayi da za a iya shiga saboda annobar coronavirus.
Dakarun tsaron kasar Amurka sun mamaye titunan Minneapolis bayan mummunar zanga-zangar da akayi ta kwanaki a jere a dalilin kisan George Floyd, wani bakin ba’amurke da ‘yan sanda suka yi. An Kona wasu gine-gine, ciki har da ofishin ‘yan sanadan.
A Najeriya, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu kauyuka 5 dake kusa da kan iyakar Niger inda suka kashe mutane da dama.
A China: 'yan jam'iyyar National Peoples Congress sun zabi aiwatar da sabuwar dokar tsaro ta Hong Kong. Dokar wadda zata rage karfin mahukuntar birnin, ta janyo suka daga kasashen duniya.
A Sudan ta kudu Wata matashiya daga Habasha, Sajen Almaz Kabtimer, ta na aikin gyaran motocin sojoji, don tabbatar da ganin dakarun wanzar da zaman lafiya na gudanart da sintiri zaman lafiya ga talakawan kasar.
A Amurka daruruwan mutane sun yi zanga zanga a Minneapolis bayan bazuwar wani bidiyo da ya nuna an sanyawa wani bakar fata George Floyd ankwa wanda daga bisani ya mutu, mintuna biyar bayan da wani dan sanda yasa kwauri ya taushe wuyarsa.
A Burundi, Shugaba mai barin gado Pierre Nkurunziza ya taya wanda zai gaje shi, Evariste Ndayish-miye (Ndayishimiye), murna wanda hukumar zabe ta ce ya lashe kashi 68.72 na kuri'un da aka kada.
Gwamnatin Afghanistan ta bukaci kungiyar Taliban da ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku wacce zata kare a daren Talata, yayin da ta sanar da sakin mambobin kungiyar 900.
Firai Ministan Japan Shizo Abe ya dage dokar ta baci ta Korona Biros a birnin Tokyo da kuma wasu sauran yankuna 4 ranar Litinin, abin da ya kawo karshen hana zirga zirga a kasar.
A Senegal kuwa musulmai da dama ne suka hadu a gaban masallacin Massalikoul Djinane don gudanar da bikin sallar Eid al-Fitr.
A Kenya Wa coci a kasar Kenya ya fito da salon gabatar da ibada da bin tituna da rukunin gidaje tare da wa’azi da kade-kade. Tun bular coronavirus gwamnati ta haramtawa coci coci budewa.
A yau Juma’a jirgin saman Kasar Pakistan ya fadi a rukunin gidaje a birnin Karaci dauke da fasinjoji 100 da hukumomi suka ce ana zaton dayawa sun mutu.
Domin Kari