A nan Amurka hukumar FBI da Ma'aikatar Shari'a na gudanar da bincike game da mutuwar wasu bakaken fata biyu a California. Tun farko dai an yi tsammanin sun kashe kansu ne, amma yanzu ana dubawa ko wariyar launin fata, ta taka rawa.
Najeriya, ta aika da sojojin gwamnati a yankin da 'yan ta'adda masu alaƙa da kungiyar IS suke, wadanda suka kashe mutane da dama a wani sabon hari.
Tun bayan bullar cutar, wasu jihohi sun ta mayar da Almajirai jihohinsu na asali, inda wasu ke cewa karshen tsarin ne yazo. Sai dai gwamman jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shaidawa Muryar Amurka cewa jihar ba ta goyon bayan tasa keyar almajiran.
Jami’ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano tana kokarin gano hanyar da za a iya yin amfani da hasken rana wajen yaki da cutar COVID19. Hukumar Jami’ar ta bayyana cewa, yana da muhimmanci ta bada gudummuwa ga yunkurin da ake yi a kasashen duniya na shawo kan annobar. Ga abinda suke yi.
U.S. : Zanga Zanga ya barke a kudancin Amurka a birnin Atlanta a daren jiya biyo bayan harbe wani bakar fata, Rayshard Brooks da ‘yan sanda sukayi a daren juma’a. Bincike da aka gudanar kan gawar ya nuna kisan gilla ne, kuma shugaban ‘Yan sandan birnin tuni ya ajiye aikinsa.
Gwamnatin Misira ta sanar da komawa harkokin sufirin jiragen sama da yawon bude idanu a kasar ranar daya ga watan Yuli amma uku daga masu saukan baki ne kadai zasu karbi baki yan yawon bude ido a wuraren sakatawa.
An soke daya daga cikin gagarumin wassanin Afirka na tseren dogon zango wanda akeyi a Ethiopia a sanadiyyar coronavirus said dai masu shirya tseren sun koma tseren ta yanar gizo domin raya wannan wasar.
A China, masu zanga-zanga sunyi bore a wata cibiyar cinikayya dake HONG KONG a rananar Jumma’a yayin da ake nuna bacin rai kan shirin China na sanya wata dokar tsaro a yankin.
A Najeriya, masu sayar da suturar gwanjo suka samu raguwar kwastomomi saboda fargabar cewa ana iya kamuwa da cutar coronavirus ta hanyar kayan da ake shigowa da su daga kasashen Asiya da Turai da Amurka.
An yankewa wani dan Iran hukuncin kisa saboda bai wa jami’an laken asiri na Amurka da Israila bayanai game da inda Qassem Soleimani yake.
Firai ministar New Zealand Jacinda Ardern ta ce kasar ta dakile cutar nan mai kisa ta coronavirus, yayin da aka sallamin mutun na karshe dake dauke da Cutar.
Tsohon shugaban wasannin tsalle-tsalle na duniya dan kasar Sanagal, Lamine Diack, zai gurfana a Kotu a Faransa, zai amsa tuhumar cin hanci da ta shafi yin rufa-rufa ga ‘yan wasan Rasha masu amfani da kwayoyi masu kara kuzari.
. Shugaban Amurka Donald Trum ya ce, ya na goyon bayan zanga-zangar lumana, amma ba zai zuba ido abin ya rikide zuwa tashin hankali ba.
Kasashe da dama na duniya sun fara sassauta dokar hana zirga-zirga da suka dauka da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19. Gwamnatoci da dama sun bayyana damuwa dangane da illar dokar kan tattalin arziki.
A Mali Dakarun kawance na G5 a yankin Sahel, sun bude wani sabon sansani don yaki da masu da’awar jihadi a Bamako, shekaru 2 bayan wani hari da suka kai tsakiyar kasar.
Amurka Masu zanga-zanga suka yi maraba da tuhumar 'yan sanda 3 da laifi bisa alaka da mutuwar bakar fata George Floyd, kana sun cigaba da zanga-zanga don neman a yi gyara ga tsarin shari'a.
A fadar Vatican, Papa Roma Francis yayi jawabi ga mabiya addini a Amurka yau Laraba, inda yayi Allah wadai da nuna wariyar launi kana ya yi kira a kawo karshen tashin hankali a kasar
‘Yan sanda a Paris na sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan masu zanga zangar mutuwar wani bakin ba-Faranse a wani aikin ‘yan sanda shekaru hudu a baya, wanda mutuwar George Floyd a Amurka ta sake tado da ita.
Domin Kari