A Amurka kuma an yiwa shugaban Trump bayani a 2019 a kan zargin Rasha ta yiwa Taliban alkawarin dukiya idan ta kashe sojojin Amurka, a cewar kafafen labarai uku a yau Talata. Trump ya musunta cewa ba a mai bayani ba.
A Senegal a wani jawabin telebijin jiya Litinin, shugaba Macky Sall, ya sanar da dage dokar ta baci da ta fitan dare a yau Talata, wasu matakan dakile yaduwar COVID-19 da kuma saukar jiragen kasa da kasa a ranar 15 ga watan Yuli.
MALAWI: Jiya Lahadi aka rantsar da sabon shugaban kasar Malawi Lazaru Chakwera, ‘yan sao’I bayan kayar da tsohon shugaban Peter Mutharika a wani zaben raba gardama da ya shiga tarihi.
CHINA: Kanfanin dillancin labaran Associated Press ta bada rahotan hukumomin Chana na tilasta yiwa matan kabilar Uighur aikin hana haihuwa da ma sauran kananan kabilu, a wani yunkuri na rage yawan karuwar kananan kabilu, tare da baiwa ‘yan kabilar Han da ke da yawa, kwarin gwiwar kara haihuwa
Wata matsala da ke ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya dangane da cin zarafin mata ita ce matsalar FYADE. Domin nuna bacin ransu da yawaitar wannan matsalar, dubban mutane ne suka fita kan tituna a manyan biranen Najeriya domin nemawa wadanda aka yi wa hakan hakkinsu.
Dr. Anthony Fauci, darektan daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka kan muhimmancin amfani da takunkumin rufe fuska, da kuma kokarin da ake yi na samar da rigakafi
A yau ne 'yan kasar ke kada kuri'a kan wani sauyi a kundin tsarin mulki da zai baiwa shugaba Vladimir Putin damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2036.
Kasar Madagaska na buki cika shekaru 60 da samun 'yanci a tsibirin, a ranar 26 ga watan Yuni shkearar 1960 tsibirin ya samu yanci daga hannun Faransa.
A Afrika ta Kudu hukumomi suka bude asibitin coronavirus na cikin wata motar vokswaja da aka daina amfani da ita, yayin da ta zama kasa ta farko a haniyar da ta fara gwajin maganin rigakafin da cibiyar Oxford Jenner Institute tayi.
A Rasha, shugaba Vladmir Putin da wasu mutane dubu 14 sun yi bukin Ranar Nasara a wani fareti a Moscow, wanda aka shriya yi tara ga watan Mayu. Faretin na zuwa kafin wani babban zaben kundin tsarin mulkin kasar da ka iya ba Putin sake yin wa’adin shugabanci sau biyu.
A Kenya, mahajar kiwon lafiya ta TIBU na baiwa mutane damar kiran likita zuwa gidansu cikin sauki. Wadanda suka kirkirota sun ce sha'awa ta karu da sauri a yayin annobar coronavirus.
A Saudi Arabiya, aikin hajji, wanda yake samun halartar musulmai miliyan biyu da rabi daga fadin duniya, za a gudanar da aikin ne wanan shekara bisa wasu sharadu, in ji ministocin Saudiyya yau Talata.
Zuhura Hassan tana kokarin kare danta yayin wannan annobar. An haifi dan Zuhura, mai shekaru biyar, da ake kira Hayyan Hamoud, da ciwon sikila. Wata matsala da take sa garkuwar jikin mutum ta yi rauni. Wannan ya jefa Hayyan Hammoud cikin hadarinkamuwa da cutar COVID-19
A Ghana kuma, masu bincike na ci gaba da nazarin magungunan gargajiya da ake gani za su taimakawa wajen yaki da coronavirus.
Yaduwar cutar coronavirus na dada karuwa a Sudan ta kudu in da yanzu ya kai kimanin mutun 1,900 ciki har da jami’an jinya 50 da wadanda suka mutu sama da 30.
Masu makoki a Birtaniya sun jera furenni a wani wurin shakatawa a Reading da aka kai harin ta’addanci. inda aka kashe mutum 3 tare da jikata da wasu da dama da yammacin asabar.
A Switzerland Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta ce an samu karuwar 'yan gudun hijira. Adadin da aka samu a shekarar bara ta kai miliyan 9, yanzu ana da adadin mutum miliyan 97.5 masu neman mafaka.
A Burundi a yau Alhamis aka rantsar da zabbabben shugaban kasar Evariste Ndayishimiye, ba yan mutuwar tsohon shugaban da ya bar kasar cikin mawuyacin hali.
Masu zanga zangar kin jinin kisan bakar fata a nan Amurka, sun cigaba da maci abirane da dama a wannan mako a kan mutuwar bakaken fatar Amurka a hannun ‘yan sanda. Masu zanga zangar sun ce mutuwar George Floyd ta kara kami ga yunkuri da aka faro shekaru da dama
A Mali shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita ya sanar cewa yana shirin kafa gwamnati bayan dubban mutane sun yi babban taro a Bamako ranar biyar ga watan Yuni suna kira ya yi murabus.
Domin Kari