Mataimakin shugaban Amurka Mike Pance, a daren jiya Laraba ya fadawa Amurkawa cewa ba za su samu zaman lafiya a hannun Joe Biden. Ya caccakin dan takarar Demokrat wanda ke neman a rage kudadden kasafi na ‘yansanda.
A Ivory Coast kuwa: Masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Lauren Gbagbo, wanda ke zaune a kasashen Turai, bayan shari’ar shi da kotun manya laifi ta duniya, sun ce zasu yankan mushi katin tsayawa takara a zaben watan Oktoba.
Wakilai daga yammacin Afirka karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, sun isa Bamako, babban birnin kasar Mali a ranar Asabar,
An soma babban taron jamiyyar Republican na kasa a Charlotte dake Arewancin Carolina. Duk da cewa ba a samu dubban mutane da suka halarci taron kamar yadda aka zata ba, wakilai ‘yan kadan za su kada kuri'u a wurin don sake amincewa da Donald Trump.
A Nijar: Shugaban kasar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, Muhammad Isuhu, ya sanar da daukar matakin tura wakilai kasar Mali, dan ganin an dawo da mulkin demokaradiyya, bayan juyin mulki.
A Amurka, Joe Biden, ya kwashe fiye da rabin karni a cikin siyasar kasar, ya amince da tikitin takarar shugabancin kasar karkashin jamiyyar Democrat a watan Nuwamba.
Kanar Assimi Goita ya gabatar da kansa a matsayin jagoran sojojin da suka hambarar da shugaban Mali, yayin da suka bai wa ‘yan kasar tabbacin cewa rayuwar yau da kullun za ta iya komawa kamar yadda aka saba daga ranar Alhamis.
A nan Amurka ‘yar takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Democrat Sanata Kamala Harris ta yi kira ga Amurkawa da su kada kuri'a, yayin da ta kafa tarihi.
A Belarus: Dubban ma'aikatan kamfanoni sun gudanar da zanga-zanga na kwanaki 9, a birnin Minsk, a ci gaba da matsin lamba ga shugaba Alexander Lukashenko don ya sauka daga mulki bayan shekaru 26
A Libiya Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas dake ziyara a kasar ya yi gargadi a game da zaman lafiya na yaudara a birnin Sirte, inda aka haifi shugaban kama karya Mohammad Gadhafi.
A New Zealand Firai Minita Jacinda Ardern ta dage zaben kasar da wata daya zuwa 17 ga watan Oktoba, yayin da har yanzu birnin Auckland ke cikin dokar kulle, saboda Korona.
A Somaliya akalla mutane 16 ne suka mutu a wani hari da 'yan kungiyar Al-Shabab suka kai jiya Lahadi, a wani Oral dake birnin Magadishu. A cewar mai magana da yawun gwamnati Ismail Mukhtar Omar.
Ambaliyar ruwa da gocewar laka yayi sanadiyyar kisan akalla mutane 16 tare da bacewar sama da mutane 600 a Sulawesi dake tsibirin Indonesiya.
Kwamandan Rundunar Sojin Somaliya Janar Odawa Yusuf Rageh, ya tsallake rijiya da baya daga wani harin kunar bakin wake da aka kai kan ayarin motocinsa ranar Litinin a Mogadishu.
Domin Kari