Zlatan Ibrahimovic Ya Tafi Jinyar Wata Bakwai

Zlatan Ibrahimovic na AC Milan

Kungiyar Milan ta ce an yi aikin kwaurin ne a Faransa, a kokarin da take yi don magance ciwon wanda ya jima yana addabar dan wasan.

An yi wa dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic aiki a kwaurinsa na hagu a ranar Laraba, lamarin da ya sa ya zama wajibi ya kwashe wata bakwai zuwa takwas yana jinya, idan har yana so ya ci gaba da taka leda a rayuwarsa ta kwallo.

Shi dai dan wasan ya kwashe wasu lokuta masu tsawo yana fama da ciwon kwaurin.

Dan asalin kasar Sweden mai shekaru 40, Zlatan ya buga wasa 23 a gasar Serie A ta Italiya, ko da yake, mafi akasari a zaune a benci.

Kungiyar Milan ta ce an yi aikin kwaurin ne a Faransa, a kokarin da take yi don magance ciwon wanda ya jima yana addabar dan wasan.

“An yi nasara a aikin, an kuma yi kiyasin cewa zai kwashe tsawon wata bakwai zuwa takwas yana jinya. In ji kungiyar kamar yadda AP ya ruwaito.

A lokacin da Ibrahimovic zai kammala jinyarsa zai kai shekara 41 kenan.

Bayan da AC Milan ta lashe kofin gasar ta Serie A a karon farko tun bayan shekarar 2011, Ibrahimovic ya ce zai ci gaba da taka leda ne kawai idan ya ji ya samu lafiya, yana mai cewa watannin da suka gabata sun kasance masu sarkakiya a gare shi.

A wannan shekara ta 2022 kwantiraginsa zai kare da kungiyar ta AC Milan.