A kokarin da Shugaba Donald Trump na Amurka ke yi na shawo kan 'yan Majalisar Dokokin tarayyar Amurka da kuma sauran Amurkawa, cewa akwai bukatar gina katanga tsakanin Mexico da Amurka, Fadar White House ta ce zai yi zaman tattaunawa kan batun tsaron kan iyaka da kuma lafiyar al'umma da yammacin yau dinnan Jumma'a.
Shugaba Trump zai tattauna ne da shugabanni a matakin jahohi, da kananan hukumomi da kuma al'ummomi.
Trump ya ce ana bukatar katangar saboda dakile kwararowar bakin haure da safarar muggan kwayoyi da kuma manyan laifuka.
Trump ya ziyarci garin kan iyaka na McAllen na jahar Texas a jiya Alhamis, inda ya ce ta yi wu ya ayyana dokar ta baci.
Yunkurin da aka yi na sasanta takaddama tsakanin shugaba Trump da 'yan Democrat a baya ya cutura, inda suka jajirce cewa ba za su ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da shi kuma ya ce ba zaib bude ma'aikatun gwamnatin da ya rufe ba.