Har ma da yadda kasashen biyu zasu yi mu’amula da juna domin tallafawa sha’anin noma da hakko ma’adanai, da kuma daukar matakan da zai kai ga karin samun nasarar yaki da ta’addanci da Najeriya ke fuskanta.
Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu, yayi karin bayani kan muhimmancin wannan ziyara. Inda yace kasashen biyu na da abubuwa a gaban su, duk da yake Afirka ta Kudu tayi fice a bangaren tattalin arziki, musamman wajen noma da hakar ma’adanai. Duk da yake gwamnatin Najeriya na ganin dogaro da Man fetur ya zama hadari, hakan yasa ta koma bangaren Noma da hakar ma’adanai. Kan wannan bututuwa ne shugabannin zasu tattauna.
Kasar Afirka ta Kudu na da manyan manyan kamfanoni dake kasuwanci a Najeriya, hakan yasa za a duba hanyar bude harkokin kasuwancin da yan Najeriya zasu ci moriya. Haka kuma Najeriya na neman taimakon Afirka ta Kudu, wajen fara kera makamai a gida.
Domin Karin Bayani.
Your browser doesn’t support HTML5