Ziyarar Shugaban Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira a Nijar

Shugaban Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ya Kai Rangadi Nijar

Shugaban hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR, Philipo Grandi, ya fara rangadi a Jamhuriyar Nijar.

Ziyarar ta talakka ne kan tantance halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a kasar musamman a yankin Tilabery inda dubban mazauna yankunan karkara suka tsere daga matsugunansu.

Grandi ya fara wannan rangadi ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kewayen garin Ouallam, a yankin Tilabery inda dubban mutanen suka tserewa hare-haren ta’addancin da aka fuskanta a makwannin baya akan iyakar Nigar da Mali.

Shugaban Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ya Kai Rangadi Nijar

Grandi ya ce, a Ouallam, na ga mutanen da suka bayyana min cewa sun yi kaura daga matsugunansu ya fi a kirga, sakamakon barazanar da suke fuskanta daga ‘yan ta’adda wadanda ke ba su umurnin su fice daga garuruwan da suke zaune.

Ya kara cewa wannan shi ne kalubale na farko da ya kamata a murkushe, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati da abokan huldarta na fannin tsaro.

Sai dai Grandi ya ce ba karfin soji kadai ake bukata ba a wannan yaki, wajibi ne ta wani bangare a dauki matakan inganta rayuwar talakawa.

Ya bayyana hakan ne a cewar shi, wadanda aka zanta da su sun fada cewa makarantu akalla 137 aka rufe sanadiyyar tashe-tashen hankula.

Shugaban Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ya Kai Rangadi Nijar

Dubban mutane ne suka gudu daga kauyukan da ke iyakar Nijar da Mali domin neman mafaka, bayan hare-haren Inates da Chinagoder.

Philipo Grandi wanda ya sanar cewa hukumar UNHCR ba za ta gaji ba wajen tallafawa ‘yan gudun hijira, ya nuna damuwa game da halin da ake ciki a kasar Mali lamarin da ya ce dole ne kasashen duniya su hada karfi don magance wannan matsala.

A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Shugaban Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira a Nijar