Yayin wannan ziyara, manyan hafsoshin sun yi alkawarin yin aiki tukuru don kawo karshen wannan matsala ta Boko-Haram a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Babban hafsan hafsoshin kasar Lucky Irabor ya samu rakiyar babbar hafsan sojan kasar Manjo Janar Ibrahim Attahiru, da babban hafsan sojan sama Air Vice Marshal Ishaka Amawo da kuma Rear Admiral Ahmed Gambo babban hafsan sojan ruwa a lokacin da ya kai ziyara fada gwamnatin jihar Borno inda suka gana da gwamna Prof. Baba Gana Zulum da kuma sanar da shi irin matakan da za su dauka na kawo karshen matsalar tsaro da hare-haren mayakan Boko-Haram a yankin.
Babban hafsan hafsoshin kasar Lucky Irabor da yake magana a fadar gwamnan, ya ce mun zo ne don mu tabbatar maku da cewa za a samu karshen ta’addancin mayakan Boko-Haram, domin za mu yi iya kokarinmu.
Ya kara da cewa suna kira ga al’ummar Borno da sauran mutan Arewa maso Gabashin kasar da su ba su dama, da hadin kai don su yi iya nasu kokarin na kawo karshen wannan matsalar cikin ikon Allah.
Ana shi jawabin shi ma gwamnan jihar Borno Prof. Baba Gana Zulum ya ce dole ne a samu hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’umma idan ana son a samu nasara.
A saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Maiduguri, jihar Borno, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.