Ziyarar Paparoma Zuwa Nan Amurka

Paparoma Francis da shugaban Amurka Barack Obama

Daruruwan Amurkawa ne daga sassan kasar daban daban suka yi dafifi domin yiwa shugaban mabiya darikar katolika marhabin a ziyarar da ya kawo Amurka irinta na farko

Fadar White House ta shugaban Amurka ce wuri na farko da Paparoma Francis ya fara yada zango a wannan ziyarar da ta zama irnta ta farko da Paparoman zai kawo nan Amurka.

Bayan zuwa White House Paparoman zai ziyarci majalisun dokokin tarayyar Amurka inda zai yi masu jawabi.

A yayin ziyarar an yiwa Pparoma Francis marhabin irin na alfarma kuma mai kayatarwa. Da yake yiwa bakon nasa marhabin shugaba Obama yace yana cike da farin cikin cewa yana yiwa bako mai dauke da abubuwa da yawa musamman abin da ya shafi tausayin marasa matsuguni zuwa wadanda yaki ya daidaita ya kaiga mutanen da basu da na cin yau balle na gobe.

Shugaba Obama yace Paparoma mutum ne mai nuna kauna ga wanda ake nunawa wariya da wadanda suke cikin halin wayyo ni Allah.

Shugaba Obama ya bayyana Paparoma Francis a matsayin jan gwarzo wanda ya dade yana taka rawa wajen ganin kasashen dake fada tsakaninsu sun sasanta domin rungumar zaman lafiya. Yace sau tari kalaman Paparoma na kokarin kyautata rayuwar mai dan karamin karfi ne da ma al'umma baki daya.

Da shugaba Obama ya tabo batun dangantaka tsakanin Amurka da Cuba sai yace ba shakka Paparoma ya taka rawar gani wajen ganin Amurka da Cuba sun mayarda huldar dake tsakaninsu. Saboda ya godewa Paparoma dangane da rawar da ya taka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Obama ya kuma tabo yadda Paparoma ke fadakar da mutane 'yancin barin kowa ya yi addininsa. Shugaban yace su a Amurka suna mutunta 'yancin addini domin ba ruwan wani da addininka saboda kowa nada 'yancin yin duk irin addinin da ya zaba musamman a irin wannan lokacin da ake kashe mutane domin kawai sun ce ga addinin da suke son su bi.

A nashi jawabin Paparoma Francis yace a matsayinsa na bako yana farin cikin zarafin baiwa masu rike da dimokradiyar kasar irin tashi shawarar da zata bunkasa rayuwar jama'a gaba daya.

Dangane da mabiya darikar katolika a Amurka kuwa Paparoma Francis yace har kullum fata da kokarinsu shi ne ganin an samarda al'umma mai juriya da sanin yakamata musamman akan abun da ya shafi 'yancin gudanar da addini.

Akan dumamar yanayi kuwa Paparoma Francis cewa ya kamata kowa ya bada tasa gudummawar domin kawo sauki ko karshen matsalar.

Yau ake kayautata zato Paparoman zai yiwa majalisun dokokin Amurka jawabi kafin ya cigaba da ziyarar zuwa birnin Philadelphia dake jihar Pennsylvania.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Paparoma Francis Zuwa Nan Amurka - 3' 34"