Ziyarar Mai Baiwa Amurka Shawara Kan Tsaro Afghanistan

McMaster

Amurka na kira ga kasashen yankuna daban-daban ciki har da Rasha da Pakistan, da kar su goyi bayan 'yan kungiyar Taliban a kokarinsu na cigaba da tsawaita dadadden yakin nan na Afghanistan.

Mai Baiwa Kasar Amurka shawara kan tsaro H.R. McMaster ne ya yi wannan kiran jiya Lahadi, bayan tattaunawarsu da shugabannin Afghanistan a ziyararsa ta farko zuwa Kabul tun bayan da ya kama aiki.

Jami'an Afghanistan sun ce tattaunawar ta ta'allaka ne kan batutuwan tsaro na bai daya, da yaki da ta'addanci a wannan banageren
da kuma karfafa sojojin Afghanistan na musamman da sauran jami'an tsaro.

McMaster ya gaya ma wata kafar labarai ta yankin mai suna TOLOnews cewa dole ne a murkushe 'yan Taliban din da su ka ki shiga tattaunawar da gwamnati ta shirya na zaman lafiya da. Ya ce Amurka ta himmatu ga karfafa sojojin Afghanistan da zummar ganin an cimma manufa.