Ziyarar Fara Ministan Japan Zuwa Tashar Jiragen Ruwan Pearl Harbor

Harin da Japan ta kai tashar Pearl Harbor

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Japan ya ce firayin minista Shinzo Abe ba zai nemi gafara game da harin da Japan ta kai kan tashar jiragen ruwan Pearl Harbor ta Amurka a shekarar 1941 ba, a ziyarar da zai kai tsibirin Hawaii a cikin watan nan.

Firayin ministan na Japan zai kai ziyarar ce don nuna kudurinsa na hangen nan gaba da kuma tabbatar da ganin bala’in yakin duniya da aka yi a baya bai sake faruwa ba, ya kuma tura sakon neman sulhu tsakanin Amurka da Japan, a cewar sakataren majalissar zartaswar Japan Yoshihide Suga, a yau Talata.
Cikin wannan shekarar za a cika shekaru 75 da kai harin da ya sa Amurka shiga cikin yakin duniya na 2.

Watanni 6 da suka gabata, shugaba Obama, ya zamo shugaban Amurka na farko dake kan mulki da ya kai ziyara zuwa wani wurin tunawa da wadanda suka mutu a birnin Hiroshima na Japan, inda a shekarar 1945 Amurka ta jefa bam din nukiliya na farko a duniya a karshen yakin da aka yi.
Mathew Linley, wani farfesa a jami’ar Nagoya, ya ce a ganin Abe da magoya bayansa dake Japan wannan ziyarar zata kawo karshen lokacin da ya biyo bayan yakin da aka yi.


A wani lamari na dabam kuma, Wani mai yiwa jam’iyyar Republican hidima a fannin manufofin hulda da kasashen waje ya isa kasar Taiwan a safiyar yau Talata a wata ziyara ta mako daya, wacce tayiwu ta hada da ganawa da shugaba Tsai Ing-wen, bayan da ta taya shugaba Donald Trump mai jiran gado murnar nasarar da ya samu ta wayar tarho ranar Jumma’ar da ta gabata.