Ranar Asabar idan Allah ya kaimu shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai amsa goron gayyatar shugaban Amurka Donald Trump, inda zai kai wata gajeriyar ziyarar aiki.
WASHINGTON D.C. —
Shugaba Buhari zai kasance shugaban ‘kasa na farko a nahiyar Afirka da zai kaiwa Trump ziyara bisa goron gayyata.
Ana kyautata zato a ganawar shugabannin biyu zasu tattauna al’amuran tsaro da cinikayya da dai wasu abubuwa makamantansu, musamman matakan da ita Amurka zata dauka wajen taimakawa Najeriya da yaki da ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa.
Muryar Amurka ta zanta da wasu kwararru a fannonin da suka hada da tattalin arziki da tsaro dakuma harkokin siyasa kan wannan ziyara ta Trump.
Domin karin bayani saurari tattaunawa ta musamman da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-HIkaya ya jagoranta a ofishin Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5