Jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce Fadar shugaban kasa ta makara a kokarin da take yi na ziyarar shugaba Muhammadu Buhari zuwa Taraba da wasu jihohi da aka samu rikici da hare-hare.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP ta ce abin damuwa ne a ce sai bayan watannin shugaban zai je wadannan wurare bayan da mahara daban-daban suka ci karansu babu babbaka.
A cewar jam’iyar ta PDP wacce ta sha kaye a hannun jam’iya mai mulki ta APC a zaben 2015 “da ma Buhari bai san damuwar talakawan Najeriya ba a daidai lokacin da suke bukatarsa.”
A yau Fadar ta shugaban kasa ta bayyana shirin ziyarar ta shugaba Buhari zuwa Yobe da Zamfara da Taraba da Rivers da aka yi fama da rikice-rikice da suka kai ga asarar rayuka da dama.
A jihar Yobe, Buhari zai kai ziyara ne saboda sace ‘yan mata da ake zargin Boko Haram ta yi a garin Dapchi makwanni biyu da suka wuce, inda suka yi awon gaba da ‘yan matan sakandaren Dapchi su 110.
Jihar Benue kuwa ta na fama ne da rikicin makiyaya da manoma yayin da a Taraba ke fuskantar wannan matsala.
Jihar Rivers kuwa ta fuskancin matsalar tsaro ne bayan da wasu ‘yan bidniga suka kashe wasu masu ibada a karshen shekarar da ta gabata.
A Zamfara kuma wasu 'yan fashin sun kai hari kan kauyen Birane inda suka kashe mutane da dama.
A yau shugaban na Najeriya zai fara ziyarar ta sa a cewar shafin Fadar shugaban kasar a sakon da ta wallafa a Twitter.