Gwamnatin ta ce ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi na kasa-da-kasa da dama, wanda hakan yasa za ta tambayi ‘yan kasar ko suna son ci gaba da kisa a zaman hukunci kan mutanen da suka aikata kisan kai ko cin amanar kasa.
Da alama kuma ‘yan kasar ta Zimbabwe suna da ra’ayoyi mabambanta kan lamarin, bisa tarukan da aka gudanar na jin ra’ayoyin jama’a.
Faston Mangezi, wani manomi ya ce “Babban muhimmi abu shi ne hana wanda aka samu da laifin kisan kai ci gaba da zama a ciki al’umma. Don haka ba sai an rataye su ba. A yi musu hukuncin da zai hana su komawa rayuwa kamar kowa.”
To sai dai Godfrey mai shekaru 39 cewa yayi, “Idan mutum ya kashe wani, tilas ne a rataye shi har lahira. Muna samun matsaloli da dama na wadanda suka yi kisan kai suna barin gidajen yari su koma a cikin al’umma, su kuma aikata irin laifin na kisan kai.”