Sa hannun da shugaban kasar Emerson Mnangagwa ya yi, ya zo ne bayan da ma’aikatan lafiya suka yi ta gwabza kazamin fada da gwamnati kan rashin albashi mai tsoka a shekarar da ta gabata.
Dubban ma’aikatan jinya da likitoci a asibitocin gwamnati a kasar da ke kudancin Afirka suka shiga yaji aiki a bara suna neman a yi musu karin albashi kana a biya su kudin yini ciki dalar Amurka sakamakon karyewar darajar kudin kasar da hauhawar farashin kayayyaki da ke mummunan tasiri ga albashin su.
Ficewar likitoci da ma’aikatan jinya ya sa asibitocin Zimbabwe ba su da isassun ma’aikata, yayin da ma’aikatan lafiya sama da dubu 4,000 suka bar kasar tun daga shekarar 2021, in ji hukumar Kula da Lafiya ta kasar a watan Nuwamban bara.
Yawancin ma’aikatan jinya a Zimbabwe suna samun kasa da dalar Amurka 100 a wata.
Reuters