Zazzabin cizon sauro na kisa fiye da yadda masana suka zata

Sauro suke cizon Bil-Adama.

Wani sabon bincike ya nuna cewa tana yiwuwa zazzabin cizon sauro tana kisa fiye da yadda wasu masana suka zata a baya.

Wani sabon bincike ya nuna cewa, tana yiwuwa zazzabin cizon sauro na kisa fiye da yadda masana suka zata a baya.

Sakamakon binciken da mujjalar kiwon lafiya ta Ingila The Lancet ta buga a ranar juma'a yace fiye da mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne zazzabin cizon sauro ta kashe a shekara ta dubu biyu da goma. Wannan zazzabi ta yiwa yara da manya barna sosai, yawancinsu a Nahiyar Afrika.

A baya an kiyasta cewa a duk shekara zazzabin cizon sauro kan kashe tsakanin mutane dubu saba'in zuwa dubu tamanin. Sabon binciken ya kuma sabawa abinda ake zato ada cewa akwai yiwuwar zazzabin cizon sauro ta kashe yara yan kasa da shekaru biyar da haihuwa fiye da manya.

An gudanar da wannan bincike ne a cibiyar nazari a jami'ar jihar Washington dake birnin Seattle arewa maso yammacin Amirka. Haka kuma bincike ya nuna cewa ana samun ragowar wadanda zazzabin cizon sauro ke kashewa a saboda mutane suna da sukunin samun magunguna da gidajen sauron da ake fesawa magani fiye da baya.

Asusun Bill da Melinda Gates ne ya dauki dawainiyar binciken.