Duk da ikirarin kokarin da gwamnatoci a Arewacin Najeriya ke cewa su na yi don kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin, ciki har da garkuwa da mutane, yaduwar makamai a hannun daidaiku, da yadda ake samar wa 'yan ta'adda bayanan sirri, da kuma yadda ake halin ko in kula da matsala tun ta na karama da dai sauransu, su aka fi mai da hankali akai a taron na wannan karon.
Aliyu Shamaki, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa rashin ilimi da cin hanci da rashawa na taka rawa a batun rashin tsaro a arewacin Najeriya, ya na mai cewa idan babu ilimi a arewacin Najeriya to an samu barakar farko akan batun kalubalen tsaro a yankin.
A nata bangaren 'yar’gwagwarmaya da ake kira da Mama Balaraba, ta yi kira ga sauran mata a yankin arewa da su fito don neman mafita ga sha’anin na tsaro.
Shi kuma Kwamred Aliyu Aminu waziri, mai magana da yawun kungiyar da ke kokarin tattauna yadda za a samu zaman lafiya a Najeria, ya ce kalubalen tsaro ba na gwamnati ne kadai ba dole sai al'umma ta sa hannu, a saboda haka yanzu suka fito da wani tsari na bin mutanen da aka saba musu kuma suka dauki makamai, za su tattaunawa da su don a samar da dorarren zaman lafiya.
Bayan nazari kan matsaloli na tsaro da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi ya sa shugabannin sashen hausa na Muryar Amurka da su ka jagoranci taron wato, Grace Alheri Abdu, Hajiya Madina Dauda da Nasiru Adamu Elhikaya fitar da matsaya kan cewa tsaro shi ne kashin bayan bunkasar tattalin arziki wanda a kullum ake kuka da tabarbarewarsa, musamman a yankunan Arewacin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5