Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Daukar Matakan Dakile Ayyukan Cin Zarafin Mata A Najeriya


Mata
Mata

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ta shirya wani taro a jihar Adamawa domin duba batutuwan take hakkin mata da kananan yara da kuma hanyoyin da za a bi domin magance irin wannan mummunar dabi’ar.

Alkalumman majalisar dinkin duniya sun nuna cewa, duk da fafutukar da kungiyoyi ke yi, har iyau ana ci gaba da samun yawaitar matsalar cin zarafin mata, musamman a kasashe masu tasowa na Afrika, ciki har da Najeriya. Wasu mata da suka taba fuskantar cin zarafi a baya sun bada labaran su a wurin taron.

A kokarin magance wannan matsalar ne yasa kungiyar Tarayyar Turai ta EU, karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya da ake kira "Spotlight Initiative" kaddamar da yekuwar yaki da wannan matsalar inda aka shirya taron tuntuba da ‘yan jarida daga wadansu sassan kasar tare da haska fitilar shirin a jihohin Lagos, Adamawa, Sokoto, Cross River, Ebonyi da kuma babban birnin tarayya Abuja inda aka ware dalar Amurka $40 million don cimma manufa.

Mrs. Shola Okpodu dake cikin jami’an shirin na Spotlight a Najeriya, tace dole ne masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wurin magance matsalolin cin zarafi da mata ke huskanta.

Tace, "duka mun hadu ne a nan domin hada karfi da karfe tare da ku ‘yan jarida don yaki da wannan matsala ta cin zarafin mata da kananan yara, wanda hakan ke nufi za mu yi aiki a wadannan jihohi da aka ambata kuma shirin na shekaru hudu ne a yanzu"

‘Yan jarida da suka halarci taron sun bayyana muhimmancin taron musamman a kasashen Afrika inda wannan matsalar tafi tsamari.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz a kan wannan taro:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG