Zauren Matasa – Tattaunawa Kan Takaddamar Zaben Wasu Jihohin Najeriya

Wani Dansanda yake bada kariya ga jami'in hukumar zabe dake tantance kayan rijistar masu zabe a Legas.

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa za’a sake zabe a wasu Jihohin Najeriya da ake takaddama, a cikin jihohin kuwa akwai jihar Taraba da Imo, hakan yasa aka bayyana cewa ranar ashirin da uku ga watan nan na Afrilu a matsayin ranar da za’a sake zabe.

Dalilin hakane Zauren Matasa ya gayyaci wasu shugabannin kungiyar matasa masu sa ido a harkar zabe a Najeriya, bakin kuwa sun hada da Abdullahi Bello da Jibril Mohammed Auwal, daga kungiyar sa ido akan harkar zabe ta Right Monitoring Group.

Abdullahi Bello ya bayyana ra’ayinsa game da dalilin dayasa za’a sake zabe a jihohin da ake mukaddama, inda yace rashin gaskiya da mutane suka nuna a lokacin zabe shine ya kawo ga bukatar sake zaben, inda ya lissafa wasu mazabu dake jihar Taraba, wanda suka ganewa kansu yadda ake sace kayan zabe da tayar da rigingimu domin hana zaben, takai ga wasu mazabu ba’a samu damar yin zaben ba.

Jibril Mohammed Auwal ya bayyana cewa kusan kowacce jam’iyya ana samun hannunta a cikin aringizon kuri’u lokacin zabe, amma mafi yawan lokaci ana samun mutane na wata jam’iyya guda ‘daya dake aikata hakan, al’ummar Najeriya sun fito sun jefa kuri’a domin nemawa kansu shugabanni nagari da suke tsammanin zasuyi aiyukan da ya kamata, amma yawancin shugabannin dake kan mulki basu son sauka daga kan mukaman su wanda hakan ke sanya mutane yin duk yadda zasuyi domin zama kan karagar mulki.