Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimiyya da Fasaha ba Kawai a Kasashen Turai ake da Itaba


Motar Tsinke
Motar Tsinke

Suma matasan Najeriya, ba’a barsu a baya ba wajen hazaka da basira da Allah ke baiwa kowane bawansa ba. Wani matashi ya kirkiri motar katafila me kwarsar kasa, wada ya kirkireta da tsinke kana kuma ya hada da wasu wayoyi, sannan yasa mata wani ingin da ake cema moto don itama ta iya kwasar kasa kamar yadda babbar motar ta ainihi keyi wajen dauka da saukewa.

Wannan bawan Allah yasamu kyautar yabo daga gwamnatin jihar Kano, domin karawa irin wadannan matasan karfin gwiwar kara hazaka.

Shida wannan matashi me suna Kamilu Adamu Sulaiman, ya samu dammar kamala karatunshi na sakandare, kuma yana da buri ya cigaba zuwa jami’a wanda yake fatar yazama babban inginiya a nan gaba. Babban abun dubawa a nan shine, matasa masu hazaka da basira yakamata su bada kaimi wajen nuna kaifin basirar su a duniya, wajen kirkiran abubuwa da zaisa kasashen Afrika su cigaba, ba sai sun dinga dogaro da kasashen yammaci ba wato turai.

Kana kuma matasa susani fa akwai irin wadannan ma’akatun a kowace jiha da suke duba irin wadannan masu hazakar don tallafa musu a kowane mataki don haka duk wani ko wata dake da wani tunanin kirkirar wani abu ko wata baiwa da Allah ya basu to su hanzarta bayyanar da kansu ko gabatar da wasu masu irin wannan basira don a taimake su kuma a samu al’uma mai nagarta da amfani wajen ciyadda ita gaba baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG