ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonakin Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 6 - Satumba 11, 2023

Nasiru Adamu

Ci gaban Zauren Matasa a garin Dan Umaru mai yawan jama'a da matasan manoma da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda suka koka da cewa ga dai damuna ta kankama amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari.

Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samar da abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Ra'ayin matasa na nuna ko dai ba za a samu yin noman yadda aka saba ba; to mutane su samu yin barci da ido biyu a rufe.

A makon jiya Umar Yakubu Farmer na bayani kan hanyoyin da ya ke ganin in an bi za a iya samun bakin zare.

Saurari shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 6 - Satumba 11, 2023