ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 5 - Satumba 4, 2023

Nasiru Adamu

Zauren matasa ya ci gaba da tattaunawa da matasa a garin Dan Umaru inda matasa da yawa ke noma a karamar hukumar Danko Wasagu dake jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda su ka koka da cewa damina ta kankama amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari.

Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samar da abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.
Ra'ayin matasan na nuna ko dai ba za a samu yin noman yadda aka saba ba, to ya kamata mutane su samu damar yin barci da ido biyu rufe.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 5 - Satumba 4, 2023