Zauren Dandali: Ya Take Ne 'Yan Mata

'Yan mata

Dandalin voa ya sami bakuncin wasu ‘yan mata ne inda suka tattauna da wakiliyat dandalinvoa Baraka Bashir akan wani sabon yayi kokuma salon sa sutura da ‘yan mata kan yi musamman abokan juna wanda a al’adance aka fi sani da shigar tagwaye, wato ‘yan mata biyu zasu sanya sutura iri guda, takalma da gyale da sauran su duk iri guda tamkar tagwaye.

Wannan sabon salo da ake kira to match, ya banbanta da yadda ake yin sa a da, banbancin sa shine mutane biyu ne zasu sa sutura iri guda wanda a da mutum guda ke sanay suturar da launinta yazo daidai da ko jakar hannu ko takalma kokuma mayafi.

Shin ko mai nene tasirin wannan sabuwar shiga da ‘yan mata kan yi a idanun al’uma?.

Ku biyo mu a shafin mu na facebook domin tofa albarkacin baki.