Zarge-zarge sun fara shiga tsakanin magoya bayan masu neman takarar shugabancin APC da ke nuna wasu ba su cancanta ba. Ba mamaki hakan hikimar rage yawan wasu ‘yan takarar ne gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar a ranar 26 ga watan nan.
Masana siyasa na kara nanata sakamakon zaben shugabannin jam’iyyar ta gwamnati, shi zai nuna irin tasiri ko akasin sa da za ta yi a babban zaben 2023. Akasarin ‘yan takarar tsoffin gwamnoni ne da duk su ka yi wa’adi biyu kan mulki inda akalla biyu daga cikin su ma yanzu haka su na majalisar dattawa.
Mafi karancin shekaru a takarar Muhammad Sa’idu Etsu ya ce duk wadanda a ka gwada a baya, ya na shagube ga tsohon gwamna Adams Oshiomhole ba su kai jam’iyyar gaci ba.
Ku Duba Wannan Ma Matasa Sun Mayar Da Taton Rantsar Da Shugabannin APC Zuwa KamfeDaya daga masu ruwa da tsaki a APC Ambasada Ali Barakat ya caccaki tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da ke cikin ‘yan takarar, ya na mai cewa ba shi da sahihiyar rijistar jam’iyyar don rashin sabuntawa bayan shigowar gwamnan Zamfara Bello Matawalle daga PDP.
Da ya ke martani shugaban APC na Zamfara bangaren Yari wato Ibrahim Birnin Magaji ya bayyana hatta rana da ya ce Yarin ya yanki takardar rijistar da karafafa cewa hakan ba zai dakatar da aniyar Yarin ba.
Zuwa yanzu dai alamu a siyasance na nuna shugabancin APC na arewa yayin da tikitin takarar shugaban kasa ka iya zama a kudu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5