Zanga-zangar Old Trafford Ta Sa An Dage Wasan United Da Liverpool

'Yan wasan Manchester United suna murnar shan kwallo, Afrilu 18, 2021.

Boren ya samo asali ne bayan da magoya bayan United suka fito don nuna adawarsu ga iyalan Glazers da suka mallaki kungiyar ta Manchester United, saboda sun goyi bayan kirkirar sabuwar gasar Super League da aka fasa.

Wata zanga-zanga da ta barke a filin wasa na Old Trafford a Ingila, ta sa an dage karawar Manchester United da Liverpool a gasar Premier League.

Boren ya samo asali ne bayan da magoya bayan United suka fito don nuna adawarsu ga iyalan Glazers wadanda su suka mallaki kungiyar ta Manchester United.

A shekarar 2005, ‘ya’yan Malcolm Glazers su shida suka saye mafi aksarin hannayen jarin kungiyar, abin da ya ba su damar mallakar kungiyar.

Masu zanga-zangar suna nuna fushinsu ne, saboda nuna goyon baya ga sabuwar da gasar Super League da aka yi, wacce aka tsara za ta maye gurbin gasar Champions League – amma daga baya aka fasa.

Rahotanni sun ce dandazon mutane ya taru a kofar shiga filin wasan na Old Trafford inda aka tsara za a fara zanga-zangar da misalin karfe 2 na rana agogon Ingila.

An dai tsara za a fara wasan na United da Liverpool ne da misalin karfe 4:30 na yamma, amma daga baya kungiyar ta United ta ba da sanarwar cewa an dage wasan da misalin karfe 5:30.

Jami’an tsaro dai sun yi nasarar korar daruruwan masu boren daga cikin filin, wanda da ma an tsara babu wanda zai shiga saboda annobar coronavirus.