Zanga Zangar Neman Ayi kwaskwarimar Zabe A Kenya

Yan Sanda Na Watsawa Masu Zanga Zanga Ruwan Zafi

Yau an wuni ana ta gudanarda tarukkan zanga-zanga a birane akalla guda ukku na kasar Kenya inda kafofin watsa labarai suka ce ‘yansanda sun bindige akalla mutum guda a garin Kisumu dake yammacin kasar.

Haka kuma ‘yansanda sun harba barkonon tsohuwa kuma suka kama wasu daga cikin jagabannin wannan zanga-zangar dake jagorancin mutane zuwa bakin harabar Hukumar Zabe da Iyakoki ta Kenya (IEBC) a biranen Mombasa da Kakamega.

A can babban birnin na Kenya kansa, Nairobi, ‘yansanda sun zagaye opishin IEBC din, kuma nan ma sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa gungun wasu masu zanga-zangar da suka auno opishin na IEBC.

Jam’iyyu da kungiyoyin ‘yan adawa dai sun lasa takobin cewa daga yanzu zasu rinka fitowa kowace ranar Litinin suna gudanarda irin wannan zanga-zangar har sai hukumar ta IEBC ta zauna da su don tattauna hanyoyin yiwa tsarin zabe kwaskwarima. A watan Agustar shekara mai zuwa ne dai za’ayi zaben shugaban kasa a Kenyar.