Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Na Shirin Daukan Matakan Dakile Yaduwar Makamai


Wani matashi rike da bindiga a birnin Monrovia na Liberiya.
Wani matashi rike da bindiga a birnin Monrovia na Liberiya.

Hukumar da ke kula da yaduwar kananan makamai ta kasar Ghana, na shirin kaddamar da wani tsari da zai wayar da kan al’umar kasar ta kafafen yada labarai, ta yadda za su farga.

Hakan na faruwa ne bayan da rahotanni suka nuna cewa wasu suna tara makamai, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamban wannan shekara.

Shugaban hukumar Jones Applerh, ya ce suna aiki kafada-da kafada da sauran hukumomin tsaro, ciki har da ‘yan sanda da masu lura da shige da ficen jama’a, domin su dakile safarar nakamai.

Ya kuma nuna takaicinsa ganin cewa wasu mambobin kungiyar kasashen bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika na ECOWAS, da suka rattaba hanu akan shirin dakile yaduwar makamai a yankin, sun gaza wajen fara gudanar da ayyukansu.

Shi dai shirin ya tanadi cewa, duk bindigar da mutum ya mallaka, sai ya yi mata rijista, sannan a ci gaba da sa ido akan bindigar tare da raba bayanai a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna, a yunkurin da ake yi na yakar ayyukan ta’addanci.

XS
SM
MD
LG