Tarzomar dai ta wakana ne akan titin Kofar mata zuwa Asibitin Murtala, zuwa yankin Shahuci, sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna Safullahi Sani dan shekaru 17 a hannun ‘yan sanda.
Mahaifiyar matashin ta fadi cewa ta yi maganar karshe da dan nata a cikin dare, har ya ce mata zai kawo mata cajin wayar shi, tun daga nan ba ta sake ganin shi ba a raye.
Shi kuwa Malam Musa Dahiru, wanda ya ke a matsayin yaya ga marigayi Saifullahi, ya ce matashin ya yi shinfida ne a kofar gidansu, ya na kallo a wayar shi, kawai ‘yan sanda suka kama shi.
Ya kara da cewa da safe ne suka samu sakon su je ofishin ‘yan sanda, don daukar gawar Saifullahi. Ya kuma ce bukatarsu ita ce a bayyana musu yadda ya samu sara a jikinsa.
Ita ma wata ‘yar uwar matashin, ta ce ba wannan ne karon farko da ‘yan sanda ke kashe musu ‘ya’ya ba, ko shekaru biyu da suka gabata sun kashe wani matashin.
Abokan matashin dai sun yi kone-kone saboda rashin adalcin da suka ce an yi mashi. Duk da cewa, mahaifiyarsa na cikin alhinin rashin danta, ta bukaci matasan da suka fusata su kasance masu bin doka da oda.
A nata bangaren, hukumar ‘yan sandan ta ce Jami’an ta sun je unguwar ta Kofar Mata rabon fada ne, tsakanin matasa ‘yan daba kuma ta musanta cewa matashi Saifullahi a hannun jami’anta ya mutu, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Kano DSP Haruna Abdullahi ya shaida ta wayar tarho.
Ga cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5