Zanga Zangar Hong Kong Ta Haifar Da Tsaiko a Tashoshin Jiragen Kasa

An dakatar da jigilar mutane a wasu tashoshin, wanda hakan yasa mutane bin dogon layi don shiga motocin bas kyauta, don isa wasu tashoshin jirgin.

Masu rajin ganin mulkin dimokradiyya ya tabbata a Yankin Hong Kong, sun kutsa zuwa cikin tashoshin jirgin kasa, inda suka hana mutane fitowa daga cikin jiragen.

An dakatar da jigilar mutane a wasu tashoshin, wanda hakan ya sa mutane bin dogon layi don shiga motocin bas kyauta, don isa wasu tashoshin jirgin.

An samu arangama tsakanin masu zanga-zanga da matafiya da ransu ya baci sanadiyyar irin tsaiko da suke kawo musu na rashin isa wajen aiki da wuri.

Sai dai zanga-zangar ta tashi daga ainihin abin da ya kawota na tun asali, na neman a dakatar da gabatar da dokar mika mutane da suka yi laifi ga kasar China don hukunta su, zuwa zanga-zangar neman kyautata mulkin dimokradiyya, da kuma kawo karshen matsi da Beijing ke nunawa yankin Hong Kong.