Wakilin mu na Legas Babangida Jibrin ya sheda mana cewar zanga zangar dalibai ta kawo cikas ga fasinjoji masu neman shiga ko fitowa daga tashan jiragen sama na Lagos.
Wasu daga cikin dalibai dake zanga zangar sun shedawa wakilin mu ta wayar tarho cewar sun rufe hanyoyin shiga filin jirgin ne domin nan ne manyan kasar ke zirga zirga, kuma hakan zai tilasta masu daukar mataki na daidaidaitawa da malaman makarantun su dake yakin aiki.
A hirar shi da Muryar Amurma, wani jami'in kanfanin jiragen sama na Max Air da baya son a ambaci sunan shi yace akasarin jiragen sama ba zasu iya zirga zirga ba, idan babu fasinjoji, saboda tsadar man jirgi, don haka zasu jinkirta tashin jirgin saman Lagos domin samun fasinjoji.
Ko a makon da ya gabata sai da dalibai suka rufe manyan hanyoyin motan data hada Lagos da Ibadan a ci gaba da zanga zangarn lumana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5