Sai dai wasu mukusantan gwamnatin ta Nijar na kallon abin tamkar wani yunkurin kwatanta abubuwan da suka faru a kasashe makwabta.
Sakin ragamar gudanar da zanga-zanga na daga cikin bukatun da shugabanin kungiyoyin fararen hula suka gabatar a yayin ganawarsu ta farkon watan nan da shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Hakan shi ne mafarin kungiyoyin suka kudiri aniyyar fitowa tituna a ranar Lahadin dake tafe a wasu biranen kasarda nufin bayyana damuwarsu akan abubuwa na ba daidai ba da suka ce suna wakana kamar yadda Maikol Zody na kungiyar Tournons la Page ya bayyana.
Sai dai a cewar Tsayabou Lawan Salao na RODDHAD, wata kungiyar farar hular dake goyon bayan gwamnati, ba za a rasa wata ajandar boye ba bayan wannan zanga-zanga a bisa la’akkari da abubuwan da suka wakana a baya bayan nan a kasashe makwafka.
Amma Maikol Zody ya tabbatar da cewa ba su da irin wannan tunani da ya sabawa mulkin dimokradiya.
Shekaru sama da 3 kenan ake ce-ce-ku-ce game da rashin samun ‘yancin gudanar da zanga-zanga a nan Nijar inda hukumomi ke bayyana dalilan tsaro da na annobar corona a matsayin hujjojin hanawa kungiyoyin fararen hula shirya jerin gwano ko gangami da makamantansu.
Hakan ya sa aka yi ta safa da marwa a kotuna saboda yadda sau tari irin wannan haduwa ke rikidewa zuwa tarzoma.
Amma bayan gabatarwa shugaban Bazoum damuwarsu akan matakin hana zanga-zanga, shugaban ya ba su tabbacin kawo karshen wannan matsala muddin suka mutunta doka.