Jami'an kiwon lafiya na Amurka sun yi gargadin cewa za a iya sake samun barkewar cutar Coronavirus sakamakon zanga-zangar kisan George Floyd da ake ta yi.
An ga masu zanga-zangar, wasu da fuska a rufe, wasu kuma ba su rufe ba, a yayin zanga-zangar da ta mamaye wasu sassan jihohin Amurka cikin ‘yan kwanakin nan.
Yin nesa-nesa da juni ya zamanto abu ne mai wuyar yi ga jama’a a yanayi na zaman lafiya, amma kuma abu ne da kusan ake ganin ba zai yi wu ba a irin wannan yanayin na zanga zanga.
"Zan ci gaba da jan hankalin jama’a da kiyaye, domin har yanzu muna cikin tsakiyar annobar. . . Har yanzu muna da asibitocin da COVID-19 ke gab da mamayewa, ”Gwamnan Minnesota Tim Walz ya fada wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press.
Hakazalika Magajiyar Garin Atlanta, Keisha Lance Bottom ta lura cewa cutar na yi wa sauran al’umomi marasa rinjaye da fararen fata ba mummunar illa.