Zanga-Zanga: Gwamnonin Wasu Jahohin Amurka Sun Bukaci Dogarawan Tsaron Kasa Su Kai Masu Dauki

  • Ibrahim Garba

Wasu wuraren da aka banka wa wuta

Gwamnonin da su ka hada da na jahar Minnesota da wasu jahohi hudu, jiya Asabar sun bukaci gudunmowa daga Dogarawan Tsaron Kasa, yayin da su ke fuskantar wani daren kuma mai cike da munanan nau’ukan zanga-zanga da mutuwar da wani bakar fatan Amurka a hannun ‘yan sanda ta haddasa.

A tsawon dare hudu da su ka gabata, zanga-zangar da aka fara cikin lumana ta rikide ta zama ta wasoso, da kone-kone da sauran wasu tashe-tashen hankula a Minneapolis da St.Paul mai makwabtaka da ita, da ma wasu biranen a fadin Amurka.

“Mu na fama da tashin hankali,” a cewar Gwamna Tim Walz wanda wannan ne wa’adinsa na farko, yana mai alkawarin cewa za a yi amfani da abin da ya kira, “cikakken karfin hukuma” wajen maido da kwanciyar hankali.

Gwamnoni a wasu jahohi hudu da su ka hada da Georgia da Kentucky da Ohio da Texas, su ma sun sa Dogarawan Tsaron Kasa cikin cikakken shiri don su taimaka wajen kwantar da hankula a wuraren da ake munanan zanga-zanga.

Magadan Gari a fadin Amurka sun kafa dokar hana fita bayan da tashe-tashen hankula su ka faru a biranensu, wadanda su ka hada da Los Angeles a jahar California; da Seattle a Washington; da Portland a Oregon; da Atlanta a Georgia; da Denver a Colorado; da Columbia a South Carolina; da Philadelphia a Pennsylvania da dai sauran biranen.