Firayim Ministan Libya yace sam, ba wata tattaunawa da zasuyi da kowa a duniya gameda wai ko shugaban Libya Muammar Ghadafi ya zauna a kasar ko ya barta, yaje wani gun.
Haka kuma Farayim Minista din, Al-Ba ghdadi al-Mahmoudi ya fada a yau cewa ba wata tataunawar arziki da zasuyi da kowa akan rikicin siyasar kasar muddin ba a ja burki ga abinda ya kira “gallazawar NATO” ba.
Firayim Ministan yana wannan kalamin ne jim kadan bayan ganawarsa da wani manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya (Abdul Elah al-Kahtib) wanda shi kuma jiya-jiya ya gama saduwa da jagabannin ‘yantawayen Libya din.
sai dai, da take maida murtani ga wadanan kalaman a birnin Brussels. wata mai magana da yawun NATO tace za’a ci gaba da fatattakar da sojan NATO ke yiwa Libya har zuwa lokacinda bukatar yin hakan ta kau.