Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da magoya bayan gwamnan ke cewa suna cike da farin ciki.
Dinbin magoya baya ne suka yi dandazo a filin was na Sani Abacha da ke Kofar mata domin shaida bikin rantsuwar sabon gwamnan.
Sadiya Dauda, wacce ke cikin ‘yan kwankwasiyya a Kano da suka kasance a filin taron, ta bayyana farin cikin da suke ciki tamkar wadanda suka halarci taron Arfa tare da nanata biyayyarsu ga tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso.
Auren zawarawa da samar da fitilun kan titi ta hanyar injinan lantarki masu amfani da man gas, daukar nauyin matasa su yi karatu a kasashen ketare, ci gaba da aikin tagwayen tituna a shalkwatocin kananan hukumomi da bai wa mata da matasa jari na daga cikin ayyuka da tsare tsaren gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso a Kano kuma sune sabon gwamnan na ya ce zai dawo dasu.
Tuni dai masana su ka fara tsokaci dangane da jawabin sabon gwamnan na Kano.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero, Kano na cewa, “Ba mu yi mamaki ba game da kalaman gwamnan na cewa zai dora kan irin ayyukan da maigidansa Rabiu Musa Kwankwaso ya bari, la’akari da cewa, matasa da sauran mutane sun zabe shi ne saboda tsohon gwamnan, wasu-ma na ganin su Kwankwaso suka zaba”
Kazalika, jawabin na sabon gwamnan na Kano ya kunshi sauke biyan haraji akan kananan ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu wadanda jarinsu bai wuce naira dubu 30 ba.
Kwamared Yahaya Shu’aibu Ungogo mai sharhi akan harkokin sana’o’in hannu da al’amuran yau da kullum na cewa, “Abu ne mai kyau, amma kamata yayi ace an gyara yadda za su rinka gudanar da sana’o’insu, kana a ba su dama su rinka biyan kudi kalilan domin su rink jin cewa, suna bada wata gudunmawa wajen tafiyar da gwamnati”
Sai dai a cewar, Farfesa Kamilu Sani fagge ga alamu akwai babban kalubale a gaban sabon gwamnan na Kano, saboda rashin kudi ga basussuka da kuma raunin tattalin arzikin Najeriya, a hannu guda kuma dinbin alkawarin da yayi Jama’ar Kano.
A yayin bikin rantsar da sabon gwamna abubuwa marasa dadi sun wakana a filin taron, inda wasu bata gari suka rinka jifar tawagar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da dan uwansa mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5