Zan Ci Gaba Da Yakar Abokanan Hamayyar Trump - Bannon

Babban mai tsara dabaru a Fadar White House shugaba Donald Trump, Steve Bannon. Jan. 28, 2017

A Fadar White ta Amurka, an sallami babban mai bai wa shugaba Donald Trump shawara a fannin tsara dabarun tafiyar da mulki yayin da gwamnatin ta Trump ke fama da suka kan rikicin da ke da nasaba da wariya wariyar launin fata da ya faru a Charlottesville na jihar virginia.

Tsohon mai tsara dabaru a Fadar White House, Steve Bannon, ya sha alwashin cewa zai daura damarar yi wa shugaba Donald Trump yaki, yayin da yake shirin komawa aiki a kafar yada labarai ta yanar gizo ta Breibart News wacce ke wallafa tsauraran ra’ayin mazan jiya.

A da Bannon shi yake shugabantar wannan kafar yada labarai, kafin ya karbi aiki a gangamin yakin neman zaben Trump da kuma gwamantinsa.

A jiya Juma’a Bannon ya bayyana hakan a wata hira ta kafar yada labarai ta Bloomberg, sa’oi kadan bayan da labarin ficewar shi daga gwamnatin shugaba Trump ya bayyana.

“Idan har akwai wani batu da ba a gane ba, bari na fayyace muku, zan bar Fadar White House, zan kuma koma na taya Trump yaki da abokan hamayyarsa da ke majalisar dokokin Amurka da kafofin yada labarai da kuma bangaren kamfanoni masu zaman kansu.” In ji Bannon a lokacin da ake hira da shi.