Nuhu Ribadu, wanda ya gaji Manjo Janar Babagana Monguno bayan ayyana shi da shugaba Tinubau ya yi a ranar 19 ga watan Yuni ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro tare da samar da daidaito a Najeriya.
Wannan al’amari na zuwa a daidai lokacin da babban hafsan tsaron Najeriya Manjo Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa rundunar tsaron Najeriya karkashin ikonsa za ta yi iya kokarinta na tattabar da maido da zaman lafiya a kasar.
Musa yayi wadanan kalaman ne, a dai dai sa’ilin da ma’aikatar tsaron kasar ta ke kokarin assasa wani ofishi da kuma ma’aikatar masana’antu na sojoji.
Nuhu Ribadu ya ce akwai gagarumin aiki a gaban gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da kasancewar Najeriya kasa daya da kuma daidaita al’amura a kasar.
Mai ba da shawara kan lamurran tsaron kasar ya ce “ wannan aikin ne da za'a yi wa ‘yan Najeriya kuma manufar mu itace mu ci gaba da aikin da aka riga aka soma."
"Za mu daidaita al’amuran kasar nan, za mu tsare kasar mu, kuma za mu samar da zaman lafiya a Najeriya domin muna da yakinin cewa lokaci yayi da kasar mu za ta ci moriyar zaman lafiya da dawo da doka da oda kamar yadda ya ke a sauran kasashen duniya" in ji shi.
Ya kara da cewa “tabbatar da ci gaba da dorewar a matsayin kasa wani abu ne da za mu ci gaba da aiki a kai. Za mu duba muga ayyukan da aka yi a baya sannan sai mu dora a kai. Domin cimma wannan manufa, za mu bukaci hadin kan ‘yan Najeriya domin samun damar gudanar da ayukan mu kamar yadda ya kamata”.