Zama Akan Teburin Sulhu Zai Kawo Karshen Takaddamar Siyasa Da Aka Shiga A Nijar?

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Masu rajin kare hakkin demokradiya sun fara jan hankulan bangarorin siyasar kasar da su hadu akan teburin sulhu don kaucewa barkewar rigingimu masu nasaba da sha’anin zabe.

Cece kucen dai ya taso a tsakanin jam’iyun siyasar jamhuriyar Nijer bayan da a makon jiya hukumar zabe ta sanar da dage zaben kananan hukumomi a dai-dai lokacin da ‘yan kasar ta Nijer mazauna kasashen waje ke guna guni sakamakon jingine nasu zaben.

Lamarin ya janyo shugaban kungiyar rajin kare demokradiya ta MPCR Nouhou Arzika ya kira taron manema labarai don jan hankulan bangarorin siyasa su yi karatun ta nutsu.

Shugaban hukumar zabe Me Issaka Sounna da ke bayani a yayin taron CNDP na bayan-bayan nan ya alakanta matakin hukumar ta CENI da yanayin annobar corona da ake ciki a duniya to amma wadansu kungiyoyin siyasa ba su gamsu da wannan hujjar ba a bisa la’akari da muhimmancin zabe a kasar.

Masana na ganin cewa zama kan teburin shawara domin samo mafitar kiki-kakar siyasar da ake fama da ita akan maganar shirye shiryen zabe ita ce hanya mafi a’ala wannan lokaci da ya rage watanni 5 a fafata.

Sabon jadawalin hukumar zabe na cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ’yan majalisar dokoki a ranar 27 ga watan Disamba kamar yadda aka tsayar a can farko yayin da tace ta dage zaben kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Nuwambar 2020 zuwa 17 ga watan Janairun 2021, matakin da jam’iyun kasar ta Nijer suka yi watsi da shi.

Saurari wannan rahoton a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Zama Akan Teburin Sulhu Zai Kawo Karshen Takaddamar Siyasa Da Aka Shiga a Nijar?