Zakara Mafi Jefa Kwallaye na 2013

Cristiano Ronaldo

An baiwa kaftin din kasar Portugal Cristiano Ronaldo kyautar yabon zama zakaran dan wasa wanda yafi kowa zura kwallaye a raga, wannan kyautar yabon dai tazone daga IFFHS wato hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa mai kula da tarihi da ‘kididdiga.

Shi dai kaftin din Portugal din ya jefa kwallaye har guda 69 a wasannin da ya buga wanda ya hada dana kulub dinsa dakuma kasarsa baki daya, wanda ya zama dan wasan da yafi kowa jefa kwallaye a raga na shekara ta 2013.

Ronaldo dai ya saka hotan sa na lokacin dayake karbar kyautar a shafin zumunta na Instagram, inda ya rubuta “ karramawa ce babba gareni kan samun kwautar zama zakaran wanda yafi kowa jefa kwallaye a raga, da hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa mai kula da tarihi da kididdiga ta bani. Nagode”

Shi dai dan wasan mai shekaru 29 yakuma fara wannan wasan kakar bani kwallon da kwazo, kuma kulob dinshi wato Realmadrid a halin yanzu sun sami nasarar cinye wasanninsu goma sha bakwai, a yau Asabar ma zasu karbi bakuncin kulob din Celta Vigo.

Your browser doesn’t support HTML5

Cristiano Ronaldo - 1'00"