Hukumar kwallon kafar, ta Turai, na bincike kan kalaman da Dan wasan gaba na Liverpool, Mario Balotelli, ya yada a, zauren sada zumunta, na Instagram, wanda yake da alaka da banbancin jinsi.
Balotelli, ya yada wani wasan bidiyo ne inda yayi masa taken “ Yi tsalle kamar bakin mutu , sa’ilin nan ya cafki kwandala kamar Bayahude”’.
Balotelli, daga baya ya cire, abun da ya yada, kuma yayi kokarin kare kansa, inda yake cewa, mahaifiyasa Bayahudiya ce saboda haka don Allah jama'a, kuyi shiru.
Daga baya yace “ Na Tuba Inda Abun da na Yada ya Bakanta Muku Rai , ban Yada shi da Niyyar Tsangwama ko Bakantawa Koya rai ba don Haka Inna mai Tuba a Gareku".
A karkashin dokar hukumar kwallon kafa idan aka same shi da laifi ana iya dakatar dashi daga buga wasani har guda biyar.