Kocin Flying Eagles Bosso Na Ruwan Ido Wurin Zabo 'Yan Wasa

Ladan Bosso-Nigeria Flying Eagles Coach

Kocin zakarun Najeriya ‘yan kasa da shekaru 20, Flying Eagles, Ladan Bosso yana fuskantar kalubale wurin zabo ‘yan wasa da zasu wakilci Najeriya a gasar cin kofin Afrika ta ‘yan kasa da shekaru 20 ta shekarar 2023.

Bosso yana da har izuwa ranar 25 ga watan Janairu ya gabatar da sunayen ‘yan wasa 21 ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, wadda ita kuma zata mika sunayen ga hukumar kwallon kafa ta Afrika wato CAF.

‘Yan wasa na cikim gida da masu taka leda a kasashen waje kowa na kokarin ganin ya samu gurbi a cikin tawagar Najeriya.

Da alama dai akasarin ‘yan wasan sun burge masu horar da su a jagorancin Bosso, wanda suke fuskantar kalubalen dake hana su bacci wurin fitar da jerin sunayen ‘yan wasa na karshe.

Flying Eagles zata fafata da kasar Zambia a wasu wasannin zumunta guda biyu da a za a yi a filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja a ranakun 27 da kuma 30 ga watan Janairu.

Kungiyar Flying Eagles da ta lashin kofin Afrika sau bakwai zata je kasar Morocco a karshen wannan wata domin gudanar da shirye shiryenta na karshe.

Flying Eagles zata yi wasa a cikin rukunin A tare da Masar mai masaukin baki, da Mozambique da kuma Senegal, a gasar cin kofin Afrika na ‘yan kasa da shekaru 20.