Zaben Najeriya: An Tafka Muhawara Tsakanin Yan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Tutar Najeriya

Kamar yadda al'adar ta ke, an tafka zafaffiyar muhawara tsakanin 'yan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam'iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa.

Da ya ke bayyana gurin muhawarar da aka yi jiya jumma’a da daddare, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi wa Jam'iyyar PDP wankin babban bargo, inda ya zargi gwamnatocin da su ka jagoranci kasar shekaru 16 cewa su su ka saka Najeriya cikin halin wahalhalun da ake ciki yanzu haka.

Osinbanjo ya kara da cewa abin da su ka fara yi a lokacin da su ka karbi mulki shekarar 2015 shi ne dakatar da barna wadda itace ta zamanto al'ada inda su ka aza tubalin kawar da talauci.

A nasa bangaren, dan takarar mataimakin shugaban kasa na babbar jam’iyar adawa ta PDP Peter Obi, ya zargi gwamnatin APC da gaza cika alkawuran da ta yi wa Jama'a, inda ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taba cewa idan su ka gaza cimma alkawuran da su ka yi wa ‘yan Najeriya to su zabi wani dan takarar a zabe mai zuwa.

Obi yace shugaban kasa kwanannan ya taba cewa matasa kowa yayi takansa, inda yace su a PDP indan aka zabe su za su kula da matasan Najeriya.

Haka dai daya bayan daya ‘yan takarar su kai ta bayyana manufofinsu da abubuwan da za su yiwa talakawa idan aka Zabe su.

Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Najeriya: 'Yan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa Sun Tafka Muhawara