WASHINGTON D.C. —
'Yan takara shidda dake gwagwarmaya a zaben shugaban kasar Mauritania, sun kammala yakin neman zaben su jiya da dare a birnin Nouakchott, bayan da kowannan su ya shirya gagarumin taron lakca ga magoya bayansa.
A karon farko tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2008, wannan ne zai zama karon farko da shugaban kasar mai ci, Mohamed Ould Abdel Aziz, zai kasance baya cikin zaben, abinda yasa kofa ta bude ga mutane da dama da ke sha’awar tsayawa zaben.
Daga cikin ‘yan takaran na yanzu har da babban madugun ‘yan adawar kasar, Sidi Mohamed Ould Boubakar, wanda ya taba rike mukamin firai-minista daga shekarar 2005 zuwa 2007.
A gobe Asabar ne dai za’a yi zaben, kuma a yi zagaye na biyu ran 6 ga watan Yuli.