Zaben Kasar Faransa Na Cigaba Da Gudana

Zaben Faransa

Sakamakon zaben kasar Faransa sagaye na biyu shi zai tabbatar da kasancewar kasar a cikin tarayyar Turai ko kuma akasin haka

Ana can ana gudanar da zaben shugaban kasar Faransa, zaben da ya fi jan hankali duniya da zafin yakin neman zabe a tarihin kasar, zaben kuma da zai yanke shawara akan ko kasar zata ci gaba da kasancewa da kungiyar kasashen turai ko kuma zata dauki wata hanyar.

Zaben da kuma yakin neman sa, batutuwan aiyukan yi da yan gudun hijira da kuma matakan tsaro suka kanainaiye. Abin dake gaban masu kada kuri’a a zaben na fidda gwani da ake yi zai kasance ko su zabi Emmanuel Macron tsohon Ministan tattalin arzikin kasar mai ra’ayin ci gaba da kasancewa cikin kungiyar kasashen turai ko kuma Marine Le Pe wadda bata kaunar yan gudun hijira.

Kididigar da aka yi kafin zaben na yau Lahadi ya nuna Mr Macron ke kan gaba da farin jinin kashi sittin da uku daga cikin dari, yayinda ita kuma Marine Le Pen take da frin jinin kashi talatin da bakwai daga cikin dari.

Yan jarida sun yi caaa akan yan takara a lokacinda suke kada kuri’arsu.