Zaben Gobe: An Koka Da Baza Sojoji a Taraba

Hadakar kungiyoyi a jihar Taraba ta koka da tura karin sojoji a jihar, saboda fargabar da mutane suka shiga a shirye shiryen zaben da za a yi gobe.

Yanzu haka hadakar kungiyoyin sa kai a jihar Taraba, ta kira taron manema labaru inda ta ce wannan mataki na tura karin sojoji a jihar yana barazana ga shirye shiryen zabe.

Wannan korafi da hadakar kungiyoyin sa kai su ka yi, ya na zuwa a lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da umarnin da shugaba Buhari ya baiwa jami'an tsaron kasar na cewa duk wanda ya saci akwatin zabe, zai iya rasa ransa.

Barrister Nerus Johnson na kungiyar Civil Society Volunteer Organization Group ya ce, yawaitar sojoji a jihar na saka fargaba da kuma ayar tambaya a wannan lokaci.

To sai dai kuma wannan ma na zuwa ne, yayin da jam'iyar APC a jihar ke zargin cewa gwamnatin PDP da ke mulki a jihar da cewa ta shirya magudin zabe ta hanyar amfani da yan Marshal, sannan kuma ta kare kalaman shugaban kasa da ake cece-kuce akai.

A martanin da gwamnatin jihar ta mayar, ta bakin hadimin gwamnan jihar ta fuskar harkokin siyasa, Abubakar Bawa ta ce, ba haka zance yake ba.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-Aziz daga Taraba:

Your browser doesn’t support HTML5

Hadakar Kungiyoyin Sa Kai Sun Koka Da Tura Karin Sojoji Jihar Taraba