Shugaba mai ci John Dramani Mahama zai yi takara ne tare da fitattun 'yan siyasa irinsu Nana Akufo-Ado na jam'iyar New Patriotic Party da Ivor Greenstreet na jam'iyar Convention People's party da sauran su.
A shirye-shiryen zaben na Ghana an jima ana rade-radin barkewar rikici a lokacin zabe, koda yake hukumomin sun musanta hakan tare da ba da tabbacin cewa za a dauki matakan tsaron.
Daga irin rahotannin da ake samu akwai cewa al'umar yankin Zango, wadanda mafi yawansu Hausawa ne, za a yi amfani da su wajen ta da tarzoma.
Amma a wata hira da abokin aikinmu na sashen Ingilishi Peter Clottey ya yi da shugaban mutanen Zango, Alhaji Baba Isah, ya musanta wannan batu na shirin ta da tarzoma:
Your browser doesn’t support HTML5