Yayin da ake ci gaba da cece-kuce dangane da batun mikawa da kuma karbar Mulki, mako guda bayan kammala zaben Amurka, manazarta a fagen demokaradiyya na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu akan darrusan da kasashe masu tasowa ka iya koya, da kuma hasashe game da manufofin shugaba Joe Biden ga Afrika.
A bayyane ya ke cewa, zaben Shugaban Amurka na wannan shekarar ya zo da al’amura na ba sabun ba a fagen demokaradiyyar kasar, kama daga yadda Jam’iyyun Republican da Democrat suka gudanar da yakin su na neman zabe, da yadda zaben ya wakana zuwa bayyana sakamakon zaben.
Alhaji Sule Lamido, wanda tsohon gwamnan jaha ne kuma tsohon Ministan harkokin wajen Najeriya, ya yi tsokaci game da darasin da kasashe masu tasowa irin su Najeriya, ya kamata su koya game da wannan al'amarin.
Ya ce Amurka ta fi Najeriya karfin tattalin arziki, da karfin soji da ilimi da kuma cigaba. Ya kara da cewa, al’adun Amurka sun banbanta da na Najeriya. Ya ce don haka darasin koyo shi ne an banbanta matuka, ta yadda babu yadda za a ce wannan zai iya amfani da tsarin wancan sosai.
Ya ce wani darasin dubuwa kuma shi ne yadda Amurka ke rigima kan addini da siyasa da kuma tsarin rayuwa sosai. Ya ce kuma ko a lokacin yakin neman zabe, wadannan banbance banbancen sun fito fili. Ya ce kamunan Amurka sun rarrabu saboda irin wadannan dalilan. Kuma haka ake yi a Najeriya, inji Sule Lamido, wanda ya kara da cewa darasin koyo mafi a’ala kawai shi ne a fahin illolin irin wadandan matsalolin a kuma yi abin da zai kawo hada kai a maimakon gaba.
Shi kuwa Farfesa Kamilu Sani Fagge dake koyar da ilimin siyasa da diplomasiyya a Jami’ar Bayero Kano, ya yi tsokaci ne akan sabbin manufofi da zababben Shugaban ka iya zuwa da su, wadanda kuma za su shafi rayuwar ‘yan Afurka.
Ya ce salon Biden na nuna alamar zai rugumi kabilu daban daban da kuma baki da ‘yan kasa. Kuma ya nuna alamar zai maida hankali kan matsakaita da kuma marasa karfi a maimakon masu hannu da shuni.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5