Bayanai dai sun nuna cewa, shugaba Buhari ya tura kudirin dokar ga ofishin babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a na Najeriya domin bashi shawara a kan wannan doka da Majalisar kasar ke bukatar ganin ya rattabawa hannu,
Jigon APC a Nigeria kuma dan Majalisar wakilan Najeriya Shele Sale Rijau yace yana mamakin yadda shugaba Buharin ke jinkirin sanya hannu a wannan kudirin doka.
Kudurin dokar dai yana bada dama ga jam’iyyun siyasa su kara yawan masu kada kuri’a a zaben fidda ‘yan takara na jam’iyyu da ake kira daliget da a ranar lahadin jam’iyyar PDP ta fara gudanar da zaben fidda ‘yan takarar ta da zasu shiga zaben neman Mukaman Majalisun jihohi.
Ku Duba Wannan Ma Shekarau Ya Fice A APC, Ya Shiga NNPPA yanzu dai masana kundin tsarin mulkin kasa na ganin matakin na shugaba Buhari tamkar tauye hakkin Damokradiyya ne kuma yana iya haifar da shari’u bayan kammala zabubbuka.
A yanzu dai ‘yan Najeriya sun zura idanu a fadar shugaban kasa domin ganin ko wannan doka zata samu shiga ko za a zuba ta a kwandon shara.
Saurari cikaken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5